ABNA24 : Taron wanda ke gudana ta kafar bidiyo, a yayinsa shugabanni da gwamnatoci da ministocin kiwon lafiya na kasashe 140 zasu tattauna kan hanyoyin biya domin murkushe annobar korona.
Taron dai na zuwa ne a daidai lokacin da wasu manyan kasashen duniya, suka bayyana anniyarsu ta yi wa mutanensu alluran riga kafin cutar a cikin makwanni masu zuwa.
MDD, dai na son a maida hankali wajen samar da riga kafin ga duniya baki daya.
Tuni dai wasu kungiyoyuin kasa da kasa suka fara nuna damuwarsu kan maganin wanda suka ce suna bukatar zurfafa bincike kan sahihancinsa, domin fadakar da jama’a ta yadda zasu karbi maganin ba tare da wata fargaba ba.
Biritaniya dai ita ce kasar farko data bayyana shirinta na fara yin riga kafin cutar, a cikin kwanaki masu zuwa, yayin da kasashen Rasha da Amurka suma suka ce sun kimsa domin yi wa mutanensu riga kafin cutar ta korona.
342/